A Watan Ramadan Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana cewa za ta haɗa wa Musulmai buɗe-baki a filin wasa na Stamford Bridge a cikin watan Ramadan mai zuwa.
Hakan yana nufin Chelsea za ta kasance kungiya ta farko a kungiyoyin Premier League da za ta haɗa buɗe-bakin na kowa da kowa tare da haɗin gwiwar gidauniyar Ramadan Tent Project.
Za’a shirya shan ruwan ne tare da hadin gwiwar gidauniyar ‘Ramadan Tent Project, wata gidauniyar taimako da aka kafa tun a shekara ta 2013 domin hade kan al’umma waje daya ba tare da nuna banbanci ba.
Kawo yanzu dai Chelsea ce a mataki na 10 akan teburin gasar firimiyar Ingila da maki 37 bayan buga wasanni 26. Sannan kungiyar ta kai matakin wasan kusa da na kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun turai.