Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alƙawarin da ya ɗauka na tabbatar da tsaro da rage talauci a yankin Arewa.
Ƙungiyar ta ce tana cike da sa ran cewa shugaba Tinubu zai cika muhimman alƙawuran da ya yi wa wannan yanki na Arewa.
Wannan na zuwa ne cikin wani saƙon taya murna ga shugaban ƙasa Tinubu da mataimakinsa Shattima kan zama shuwagabannin Najeriya da suka yi.
Wannnan saƙo ya samo saka hannun daraktan yaɗa labarai da wayar da kai na ƙungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, wanda ya ce ƙungiyar na amfani da wannan dama ne wajen tuna wa shugaban ƙasa wasu daga cikin alƙawuran da ya yi wa yankin na Arewa da suka haɗa da magance matsalar tsaro da tabbatar da adalci da rage talauci.
A ƙarshe ƙungiyar ta ba wa shugaban ƙasar tabbacin yin aiki tare da shi wajen taimaka masa wajen cika wa ‘yan Arewa alƙawuran da ya ɗaukar musu.