222 Sakataren Kungiyar Fafutikar Sake Farfaɗo da Arewa Dokta Salisu Nani Zigau, ya ce suna goyon bayan shirin zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Najeriya.
Da ya ke magana da yawun ƙungiyar, ya ce suna da yakinin cewa matakin wannan zanga-zanga da ke tafe zai kawo sauyin da ake matukar buƙata a Najeriya a halin yanzu.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, Dokta Salisu Nani Zigau, ya bayyana cewa dokar kasa ta ba ’yan Najeriya ’yancin yin zanga-zanga, kuma babbar dama ce gare su ta bayyana buƙatunsu da neman adalci da kuma kawo kyakkyawan sauyi a al’amuran yau da kullum.
Ya ce, “Zanga-zangar lumana da ake shirin yi a fadin Najeriya shaida ce da ke nuna ittifaki da kuma jajircewar ’yan Najeriya domin sama wa kansu da kuma ’ya’yansu ingantacciyar rayuwa a nan gaba.
“Ba sai mun ɓata lokacin bayyana muhimmancin wannan zanga-zanga a yankin Arewa ba.
“A tsawon lokaci, yankin Arewa na fama da matsalolin talauci da rashin tsaro da ta’addancin Boko Haram.
“Sauran sun hada da rashin abubuwan more rayuwa ga kuma tarin yara da basa zuwa makaranta,”
Sakataren ya ci gaba da cewa, “Wannan zanga-zangar wata dama ce ga ’yan Arewa su hadu su nuna rashin jin dadinsu da kuma bukatunsu musamman na samun shugabanci na gari da kyawawan tsare-tsare da za su daga daraja da yanayin rayuwarsu da na yankin.”
Ya ƙara da cewa, “muna kira ga masu wannan zanga-zanga su kasance cikin lumana da bin doka.
“Sannan muna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da kungiyoyin fararen hula da su mutunta ’yancin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba masu zanga-zangar na bayyana ra’ayinsu da rashin jin daɗinsu ta hanyar lumana.
“Muna ƙira ga gwamnati ta saurari buƙatunsu ta biya musu sannan ta ɗauki matakan share musu hawaye tare da tafiyar da kowane bangare”
Dokta Salisu Nani Zigau ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su haɗa kansu, inda ya ce,
“Ya kamata mu yi amfani da wannan dama mu hada kanmu matsayin ƙasa guda domin samun rayuwa mai inganci a nan gaba.”