Ɗalibar Jami’ar Tarayya ta Gusau Zarah Abubakar Shehu, ƴar shekaru 21 ta rasu a hannun masu garkuwa da mutane bayan ta kwashe watanni huɗu a tsare.
Zarah, wacce dalibar aji na 3 ce, an sace ta daga gidansu da ke unguwar Damba a Gusau da sanyin safiyar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, shekarar 2024, lokacin da ‘yan bindiga suka farmaki yankin.
Da farko masu garkuwar sun bukaci a biya su naira miliyan 35, amma daga baya an cimma matsaya kan naira miliyan 10.
- Shugaba Tiani Ya Jagorancin Ɗaga Tutar Ƙungiyar AES
- FRSC Ta Kama Motoci Sama Da 350 Da Lambobin Jabu
Duk da haka, bayan an biya kudin fansa, masu garkuwa sun ki sakin Zarah. Sun bukaci a kawo musu babura hudu (Boza) da katon hudu na man inji kafin su sake ta
Bayan watanni ana kokarin cika wadannan bukatu, an samu damar samar da kayayyakin da suke so.
Amma da aka sanar da shugaban masu garkuwa, sai ya kira mutanensa, inda suka bayyana cewa Zarah ta mutu kuma an binne.
Zarah ita ce ‘ya mace guda tilo ga mahaifiyarta, kuma ta shafe watanni huɗu a hannun masu garkuwa da ita.