Iyayen gwarzon gasar karatun Alkur’anin da aka sace a Katsina Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa a Jihar Katsina, sun bayyana cewa sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
An sace Abdulsalam, wanda ya lashe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Kebbi tare da mahaifinsa ne makonni biyu da suka gabata, bayan Gwamnan Katsina Mal Umaru Dikko Radda ya karrama shi.
Mahaifinsa, Malam Rabiu Zakariya Faskari, ya shaidawa manema labarai cewa suna tsare a hannun ’yan bindiga a Katsina har sai da wani babban ɗan bindiga mai suna Yellow daga Zamfara ya zo ya karɓe su da ƙarfi.
- Hana Ɗangote Mai A Naira Ya Tashi Farashinsa A Najeriya
- Cikin Hotuna: Yadda Hukumomin Tsaro Suka Yi Shirin Bayar Da Tsaro A Kano
“Ya yi wa masu garkuwa duka kafin ya tafi da mu,” in ji shi.
Ya ce an yi ciniki kan fansa amma Yellow ya ƙi yarda.
“Muna ta addu’a har ranar Juma’a da aka zo aka ce mu fito mu tafi. Yaransa suka ɗauke mu suka kai mu wani gari, daga nan muka yi tafiyar awa huɗu kafin muka samu mota.”
Malam Rabiu, ya ce da suka hau babur sai direban ya shaida musu cewa an kashe Yellow.
“Ashe mutuwarsa ce ta sa yaransa suka sake mu muka koma gida.”