Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Alhaji Aliko Dangote ya kai ziyarar ta’aziyya gidan tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya kuma mamallakik tashar MUHASA Muhammad Babandede OFR, OCM bisa rasuwar Mahaifiyarsa Hajiya Hajara Muhammad.
Ɗangote ya ziyarci Babandede ne a gidansa da ke brinin Kano kwanaki shida bayan rasuwar.
Yayin ziyarar ta’aziyyar, Ɗangote ya yi addu’ar Allah ya gafartawa Hajiya Hajara, ya ce rashin ta ba iya iyalanta ya shafa ba, lura da cewa ta raini mutane da yawa.
- Dalilan da Suka Sanya Abba Ibrahim ya Lallasa Isaaka Isaaka Awasan Kokawar Kasar Nijar a Jihar Dosso.
- An Kama Mai Kai Wa Turji Makamai
Alhaji Aliko Dangote ya kuma hori iyalanta da suyi koyi da managartar halayenta.
Ya yi adduar Allah ya basu hakuri domin jure wannan babban rashi da akayi.
Da yake karbar gaisuwar, Muhammad Babandede ya godewa Alhaji Aliko Dangote da wannan taaziya, tare da yi Masa addu’ar Allah ya maida shi gida lafiya.