Ƙarin ayyukan alheri ga Kanawa na nan tafe ~ gwamnan Kano

Gwamnan Kano ya jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da ayyuka da za su inganta rayuwar al’umma.

Gwamnna ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar zartawas karo na 7 a gidan gwamnati, inda ya yi alƙawarin cewa akwai ayyuka masu yawa da za su zo nan ba da daɗewa ba.

Wannan na zuwa ne bayan rabon kayan tallafin rage raɗaɗin man fetur, inda gwamnatin ta raba shinkafa da masara a mazaɓu 484 da ke faɗin jihar nan.

Sannan gwamnan ya ce tuni gwamnatinsa ta ƙaddamar da rabon kayan makaranta na koyo da koyarwa, da kayan makaranta da jakunkuna da takalman zuwa makaranta da sauransu.

Baya ga wannan gwamnan ya ce auren gata da aka yi da raba jari da tura ɗalibai ƙasashen waje duk wasu ma’aunai ne, a cewar gwamnan da za su tabbatar wa da al’ummar jihar nan irin kyawawan manufofin gwamnatinsa.

A ƙarshe, gwmanan ya gode wa al’ummar jihar nan kan irin goyon bayan da suke ba shi da kuma addu’o’i tare da yaba wa ‘yan jarida kan irin gudunmowar da suke ba wa gwamnatinsa.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr