Ƙasar Angola Ta Ƙwace Matsayin Najeriya Wajen Fitar da Gangar Mai a Afirka

Adadin danyen man da Najeriya ke hakowa ya ragu zuwa ganga dubu dari 9 da 99 a kowace rana a watan Afrilu, lamarin da y aba wa Angola damar shiga gaban Najeriya.

Ƙasar  Angola na samar da gangar man fetur miliyan 1 da 63 a kowace rana.

Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton wata-wata da aka fitar a watan Afrilun makon da ya gabata na kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai fetur.

Najeriya ta yi asarar gangunan danyen mai dubu 270 a watan Maris, kamar yadda alkalumman kungiyar OPEC din suka nuna.

OPEC ta ce gaba daya, mamboninta 13 na samar da gangunan mai miliyan 28 da dubu 60 a kowace rana a cikin watan da aka yi la’akari  da shi wajen yin wannan rahoto.

Sannan rahoton ya ce an samu karuwar danyen man da ake samarwa a Sudiyya, Angola da Iran, a yayin da aka samu akasin haka a Iraq da Najeriya.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro