Jihar Fulato: Mutane 85 Sun Sun Mutu a Rikicin Makiyaya da Manoma

Mahukunta sun tabbatar da mutuwar mutane 85 cikin kwanaki da aka kwashe ana rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato da ke Arewa Maso Tsakiyar ƙasar nan.

Rikicin ya ɓarke ne tun a ranar Litinin a yankin da ake yawaita samun rikicin ƙabilanci da addini a tsawon shekaru.

Har yanzu dai babu wasu sahihan bayanai da ke tabbatar da ainihin abin da ya hadasa rikicin.

Irin wannan rikici tsakanin makiyaya da manoma domin ɗaukar fansa abu ne da aka saba gani a kauyuka da dama da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Hukumar agajin gaggawa ta jihar wato SEMA ta ce rikicin ya raba dubban  mutane da muhallasu.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro