Kenya ta hana taron jama’a saboda cutar Ebola

Ƙasar Kenya ta dakatar da gudanar da tarukan gwamnati da tarurruka a cikin otal-otal bayan ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola.

Jami’an lafiya sun ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na dakile yaɗuwar cutar.

A cewar hukumomi, mutumin da ya kamu da cutar, wanda ɗan ƙasar Kenya ne, ya rasu a ranar Litinin bayan ya yi tafiya daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ta cikin ƙasar Uganda kafin ya isa Kenya.

Hukumomin lafiya sun ce suna ci gaba da ɗaukar matakan kariya da sa ido domin hana yaduwar cutar zuwa wasu yankuna na ƙasar.

Post masu alaƙa

Hukumomin Nijar sun tabbatar da tsare ɗan jarida Moussa Kaka

‘Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami’

Gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium