Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutum 48 da aka yi garkuwa da su bayan sun fatattaki ’yan bindiga da suka kai hari ƙauyen Magami da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara.
Sojojin sun ce sun samu kiran neman agaji da sanyin safiyar Lahadi cewa wasu ’yan bindiga masu yawa, a kan babura 40, sun kai hari ƙauyen tare da yin garkuwa da mutane da dama.
A cewar rundunar, sojojin sun isa wajen tare da fafatawa da ’yan bindigar.
An ceto dukkanin mutane 48 da aka yi garkuwa da su.
Sai dai mutum ɗaya ya rasa ransa yayin harin, yayin da wasu mutum biyu suka samu raunukan harbin bindiga.
An kai su Babban Asibitin Kaura Namoda domin samun kulawar likitoci.
Bayan ceton mutanen, sojojin sun ci gaba da sintiri a yankin domin hana sake kai hare-hare da kuma ƙarfafa tsaro.
Rundunar ta yaba wa sojojin bisa jarumtaka da ƙwarewar da suka nuna.
Haka kuma ta buƙaci mazauna yankin su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma