Kotu Ta Yankewa Ummin Mama Hukunci Saboda Yada Badala A Tiktok

 

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta, a hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta yankewa Rukayya Ibrahim wadda akafi sani da Ummin Mama, hukuncin daurin watanni bakwai a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya ko zabin biyan tarar naira dubu hamsin, saboda da samun ta da laifin yada tsiraicinta a shafin Tiktok da tayar da tarzoma da kuma lalata tarbiya a kafofin sada zuminta.

 

Tunda farko, Muhasa TV da Radio 92.3 FM, ta ruwaito muku cewa hukumar hisbah ta jihar Kano ce ta kama Ummin Mama, a cikin gidan namun daji dake Zoo road, daga bisani kuma hukumar, ta miƙa ta ga ƴan sanda su kuma suka cike mata takardun tuhuma tare da gurfanar.

Matashiyar Ruƙayya Ibrahim, ta ce da zarar ta fito daga gidan yarin wa’azi za ta koma yi a shafukan sada zumunta sanye da Hijabi, duba da wahalar da ta sha a gidan yarin.

 

Idan ba a manta ba Muhasa TV Radio 92.3, ta ruwaito muku cewa, Wani mutum ya Yi wa alkalin dake Sauraren shari’ar ta yin bashi Dalolin Amurika don ya saki yar TikTok din, amma alkalin kotun Sani Tamim Hausawa yayi fatali da tayin cin hancin .

Post masu alaƙa

Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika

Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari