Rundunar yan sandan jihar Kano, ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin kisan gillar da aka yi wa wata matar aure mai suna, Ruma Sha’aibu yar shekaru 24, a yankin unguwar Alhamis – Farawa karamar hukumar Kumbotso ta jihar.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu rahoton mara dadin ji, daga mijin ta mai suna Ibrahim Muhammed, wanda ya dawo gida ya tarar da matar tasa kwance cikin jini da wuka a jefenta.
Wannan mummunan al’amurin ya faru a ranar Lahadi da misalin karfe 2:45pm bayan mijin marigayiyar ya fita daga gida da misalin karfe 2:00pm na rana don kai Babur dinsa wajen mai faci, kuma acanne ya dinga kiran wayar matar tasa amma bata shiga ba, har ya kira makociyarsu don ta bincika masa ko bata kusa da wayar ta, amma ita ma tazo ta kwankwasa gidan bata ji motsin kowa ba.
Daganan ne mijin matar ya dawo don bincika wa inda ya ganta kwance cikin jini, an yi mata yankan rago, lamarin da ya dugunzuma rayuwarsa da ta dangin marigayiyar wadanda dukkansu yan uwan juna ne da aka yi musu auren zumunci.
- Zanga-zangar Adawa Da Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Barke A Abuja Da Legas
- ‘Yan Sandan Najeriya Sun Janye Gayyatar Sarki Muhammadu Sunusi II
SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa, an samu marigayiyar kwance cikin jini da raunuka da kuma yankan da aka yi mata a wuyanta.
Dangin marigayiyar sun roki mahukunta a dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka samu da laifin kisan yar uwar tasu, domin basu bata tsintar kansu cikin irin wannan hali ba , da aka sanya su cikin damuwa.
Rundunar yan sandan ta ce kawo yanzu bata kama kowa ba, amma kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na kwakwaf don kamo dukkan wanda yake da hannu a wannan aika-aika don daukar matakin shari’a akansu.
Ruma, ta rasu tana dauke da juna biyu , kuma tuni aka yi janazar marigayiyar kamar yadda addinin musulinci ya tanadar.