2027: Sarkin Gumel Alhaji Dr. Lawan Ahmad Muhammad Sani, Ya Tabbatar Wa Namadi Da Kuri’un Al’ummar Masarautar

Daga Ali Rabiu Ali, Dutse

Sarkin Gumel, Alhaji Dr. Lawan Ahmad Muhammad Sani, ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, cewa al’ummar masarautar Gumel za su ba Jam’iyyar APC gagarumar nasara a zaɓen shekarar 2027, yana mai bayyana gwamnan a matsayin ɗan gida a masarautar.

Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026, yayin bikin ƙaddamar da aikin kashi na huɗu na hanyoyin cikin garin Gumel, tare da ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen APC na shiyyar Gumel na shekarar 2027.

Ya ce alaƙar da ke tsakanin gwamna Namadi da al’ummar Gumel ta wuce siyasa, duba da irin ayyukan raya ƙasa da gwamnan ya gudanar a yankin, baya ga kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da masarautar.

A cewarsa, cikin shekaru uku kacal, gwamnatin jihar da ta tarayya sun aiwatar da ayyuka da dama a Gumel da kewaye, waɗanda suka taimaka wajen inganta rayuwar al’umma.

Sarkin ya lissafa kafa cibiyar bayar da maganin wanke ƙoda kyauta, gina hanyoyin cikin gari, sanya fitilun hasken rana a kan tituna, kamfanin sarrafa amfanin gona na Maigatari da kuma kamfanin ƙera na’urorin hasken rana a Maigatari a matsayin wasu daga cikin muhimman ayyukan da aka gudanar.

Ya ce ayyukan sun yi yawa da ba zai iya ambaton dukkaninsu ɗaya bayan ɗaya ba, yana mai cewa al’ummar Gumel na yaba wa gwamnatin Namadi bisa irin wannan ƙoƙari.

“Ba zan iya ambaton dukkan ayyukan da Malam Umar Namadi ya gudanar a Gumel ba. A cikin shekaru uku kacal, mun ga ayyuka masu muhimmanci a fannoni daban-daban,” in ji Sarkin.

Ya kuma tuna yadda gwamna Namadi ya nuna kulawa da taimako a lokacin da mahaifinsa ke fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa, tare da irin goyon bayan da ya samu a lokacin da ya zama sabon Sarkin Gumel.

A cewarsa, waɗannan kyawawan halaye da kulawar da gwamnan ya nuna ba za su gushe daga zukatan al’ummar masarautar ba.

Sarkin ya yi kira ga al’ummar Gumel da su ci gaba da bai wa APC goyon baya, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2027.

A nasa jawabin, Gwamna Malam Umar Namadi ya bayyana farin cikinsa bisa yadda dubban magoya bayan APC suka fito domin tarbarsa a Gumel, yana mai cewa yawan mutanen ya wuce yadda ya yi tsammani.

Ya ce taron ya nuna irin karɓuwar da APC ke da ita a Jihar Jigawa, tare da nuna shirin al’ummar jihar na bai wa jam’iyyar goyon baya a zaɓen 2027.

“Alhamdulillah, yau a karon farko mun zo nan Arewa maso Yamma, kuma mun ga irin wannan taro mai yawa na al’umma. Wannan ya nuna cewa Jihar Jigawa ta APC ce, APC kuma ita ce Jigawa,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa irin wannan fitowar jama’a alama ce da ke nuna cewa al’ummar Jigawa a shirye suke su zaɓi APC daga sama har ƙasa.

Da yake magana kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamna Namadi ya ce ya isar da saƙon shugaban ƙasa ga al’ummar jihar, musamman dangane da wani sabon shiri da gwamnatin tarayya ke yi domin tallafa wa manoma.

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kafa wani kwamiti nan take domin samar da tsarin da za a riƙa sayen amfanin gona daga manoma a farashi mai tsoka, ta hanyar samar da rumbunan ajiya na musamman.

A cewarsa, shirin zai ba manoma damar kai amfanin gonarsu zuwa waɗannan rumbuna domin gwamnati ta saye su a farashin da ya fi wanda ake samu a kasuwa.

“Mai girma shugaban ƙasa ya kafa kwamiti nan take domin tabbatar da cewa za a samar da rumbunan ajiya inda manoma za su riƙa kai amfanin gonarsu, kuma a saye su a farashi mai tsoka,” in ji Namadi.

Gwamnan ya ce wannan mataki zai ƙarfafa manoma, ya inganta samun kuɗaɗensu tare da ƙara bunƙasa harkokin noma a jihar.

Ya gode wa Shugaba Tinubu bisa wannan shiri, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kai saƙon ga manoma a matakin ƙauyuka domin su fahimci yadda za su amfana da shirin.

A nasa jawabin, Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Hamisu Muhammad Gumel, ya bayyana Gumel a matsayin yanki mai ƙarfi ga APC, yana mai godiya ga Sarkin Gumel da al’ummar yankin bisa irin ƙauna da kulawar da suka nuna wa gwamnan.

Ya ce irin tarbar da aka yi wa gwamnan ta nuna cewa al’ummar Gumel sun riga sun zaɓi APC a zukatansu gabanin zaɓen 2027.

Hamisu ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ayyukan raya ƙasa da kuma tallafa wa matasa a Gumel da sauran ƙananan hukumomin jihar.

Ya ce gwamnati na da ƙudirin inganta rayuwar matasa da mata ta hanyar shirye-shiryen da za su samar musu da damammakin dogaro da kai, bunƙasa sana’o’i da inganta tattalin arzikinsu.

Ya kuma buƙaci al’umma su ci gaba da ba gwamnati haɗin kai domin samun nasarar aiwatar da shirye-shiryen ci gaba.

Shi ma a nasa jawabin, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Hon. Sani Isya Gumel, ya bayyana al’ummar Gumel a matsayin mutane masu sanin darajar alheri, waɗanda ba sa mantawa da duk wanda ya kyautata musu.

Ya yaba wa al’ummar bisa irin goyon bayan da suka nuna wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Umar Namadi, yana mai cewa hakan ya nuna cewa alaƙar da ke tsakaninsu da shugabannin ta ginu ne bisa amincewa da kuma gamsuwa da ayyukan da suke yi.

Ya ce taron jama’a da aka gani a wajen gangamin ya nuna irin yadda al’ummar yankin suka amince da jagorancin APC.

Mataimakin Kakakin ya yi kira ga al’ummar masarautar Gumel da su tabbatar da cewa sun zaɓi APC a dukkan matakan zaɓen shekarar 2027.

Wakilin mu Ali Rabiu Ali ya rawaito cewa an gudanar da taron ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na ci gaba da inganta ababen more rayuwa, tare da ƙaddamar da shirin yaƙin neman zaɓen APC na shekarar 2027 a shiyyar Gumel.

Taron ya samu halartar shugabannin gargajiya, jami’an gwamnati, ’yan siyasa, shugabannin jam’iyya da dimbin magoya bayan APC daga sassa daban-daban na masarautar.

Post masu alaƙa

Ba za mu lamunci tada zaune tsaye ba a yayin tarukan siyasa—Tinubu

Tinubu zai ƙaddamar da titin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Kano a watan gobe

Atiku ya yi zargin ƙoƙarin hana shi takara a 2027 saboda kasancewarsa ɗan Arewa