• Home  
  • Sarakunan Arewa Sun Koka da Dambarwar Masarautar Kano
- Labarai

Sarakunan Arewa Sun Koka da Dambarwar Masarautar Kano

Majalisar sarakunan arewacin Najeriya ƙarƙashin mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar lll, ta nuna damuwarta kan halin da ake ciki a Kano kan rikicin sarauta. Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin hadin kan sarakunan arewacin ƙasar, wanda kuma shi ne sarkin Gummi, Alhaji Lawal Hassan […]

Sarkin Musulmi

Majalisar sarakunan arewacin Najeriya ƙarƙashin mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar lll, ta nuna damuwarta kan halin da ake ciki a Kano kan rikicin sarauta.

Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin hadin kan sarakunan arewacin ƙasar, wanda kuma shi ne sarkin Gummi, Alhaji Lawal Hassan Gummi, ta ce rikicin ka iya shafar tsarin sarauta a yankin.

Haka kuma Majalisar ta yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, a jihar Kanon.

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi ll kan karagar sarautar Kano bayan majalisar dokokin Kano ta yi wa dokar masarautun jihar kwaskwarima.

Sai kuma wata kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da dokar, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin sauraron shari’ar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai