• Home  
  • ‘Yan Sandan Najeriya Sun Fara Aiwatar Dokar Inshorar Motoci
- Babban Labari - Labarai

‘Yan Sandan Najeriya Sun Fara Aiwatar Dokar Inshorar Motoci

Benjamin Hundeyin, ya ce wannan shirin na inganta insharar motoci zai tabbatar da cewa masu motoci masu bin tituna sun sami kariya.

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Mai magana da yawun ‘yan sandan Najeriya a Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce wannan shirin na inganta insharar motoci zai tabbatar da cewa masu motoci masu bin tituna sun sami kariya.

‘yan sandan ya ce aiwatar da dokar, wanda aka fara a Legas a ranar Asabar, na bin umarnin Sufeto-Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, wanda ya bukaci a tabbatar da cewa duk masu ababen hawa sun mallaki inshorar motocin mai inganci.

Ya bukaci direbobi da masu ababen hawa su bi doka da oda, yana mai cewa wadanda suka saba za a hukunta su.

Mai magana da yawun ‘yan sanda ya kuma bukaci jami’an da ke aiwatar da dokar su nuna kwarewa a yayin gudanar da aikinsu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai