• Home  
  • An Kashe Shugaban Jam’iyyar APC A Ondo
- Babban Labari - Labarai

An Kashe Shugaban Jam’iyyar APC A Ondo

Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ose ta jihar Ondo, Nelson Adepoyigi. Clement Kolapo Ojo, shugaban karamar hukumar Ose, ya tabbatar da mutuwar Adepoyigi a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Lahadi. Ojo, a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Oluwaseun Ogunniyi ya sanya wa hannu, […]

Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ose ta jihar Ondo, Nelson Adepoyigi.

Clement Kolapo Ojo, shugaban karamar hukumar Ose, ya tabbatar da mutuwar Adepoyigi a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Lahadi.

Ojo, a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Oluwaseun Ogunniyi ya sanya wa hannu, ya ce ‘yan bindigar sun kashe shugaban jam’iyyar APC din ne bayan an sako wadan da suka kai kudin fansar ga ‘yan fashin da a baya aka rike a daji. 

“Muna godiya ga Allah da ya dawo mana da  wadan da suka yarda sukai kudin fansar, abin bakin ciki ne matuka, yadda aka kashe shugaban jamiiyya, akwai raɗaɗi sosai yadda masu garkuwa da mutane suka halaka Mista Nelson Adepoyigi.

“Daukacin shugabanni da al’ummar karamar hukumar Ose suna alhini da wannan babban rashi, muna mika sakon ta’aziyyarmu ga ‘yan uwa da abokan arziki da kuma ‘yan siyasa”.

Sai dai duk kokarin da manema labarai suka yi basu samu jin ta bakin Mista Wilfred Afolabi, kwamishinan ‘yan sanda a jihar Ondo ba. 

Sai dai wani babban jami’in ‘yan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa maneman labarai cewa, a halin yanzu tawagar jami’an tsaro a jihar na cikin daji suna neman gawar Adepoyigi.

Ya ce “Eh, gaskiya ne an kashe mutumin, amma mutanen mu suna cikin daji, suna aikin gano gawarsa,” in ji shi. An yi garkuwa da Mista Adepoyigi a garin Ifon da yammacin ranar Litinin a kofar gidansa da ke kan titin Ifon/Owo.

Tun da farko dai wadanda suka sace shi sun bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 100 domin su sake shi kafin a sasanta da iyalansa kan Naira miliyan biyar.

Amma a cikin wani yanayi mai ban mamaki, ‘yan fashin sun tsare wadan da suka kai kudin fansar biyu -Bayode Loco da Isimeri a ranar Laraba da tsakar dare.

‘Yan bindigar sun sake neman Naira miliyan 30 domin su sako mutanen uku da suka hada da Adepoyigi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai