• Home  
  • Kungiyar Malaman Jami’ar jihar Yobe Ta Janye Yajin Aiki
- Babban Labari - Labarai

Kungiyar Malaman Jami’ar jihar Yobe Ta Janye Yajin Aiki

Ƙungiyar malaman jami’a reshen jami’ar jihar Yobe sun sanar da janye yajin aiki da suka shiga ranar 11 ga watan Yulin, 2025. Shugaban malaman jami’ar, Ahmed Karange, ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar ta Yobe, inda ta yi alkawarin biyan sauran buƙatu da malaman ke nema. “Bayan cimma yarjejeniyar, shugaban malaman jami’ar […]

Ƙungiyar malaman jami’a reshen jami’ar jihar Yobe sun sanar da janye yajin aiki da suka shiga ranar 11 ga watan Yulin, 2025.

Shugaban malaman jami’ar, Ahmed Karange, ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar ta Yobe, inda ta yi alkawarin biyan sauran buƙatu da malaman ke nema.

“Bayan cimma yarjejeniyar, shugaban malaman jami’ar ya bayar da damar janye yajin aikin,” kamar yadda sanarwar da suka fitar ta bayyana.

Sanarwar ta buƙaci dukkan mambobi da su koma bakin aiki nan take

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai