Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari.
Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa, Kodayake babu asarar rai.
Bayan dawowar tsohon ministan a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gida ya yi zargin siyasa ce ta a da aka kai masa harin, yana mai jaddada cewa, harkar siyasarsa babu gudu babu ja da baya.
“Shari’a ta tanadi ka kare kai, in aka kawo maka hari amma kai kar ka kai wa kowa hari, maganar siyasa ba gudu ba ja da baya.
“Muna da hakkin kare kai in an ture mu, kariyar kai a shari’ar Musulunci hakki ne, mai girma Gwamna ya ce ya bude littafin siyasa mu ko mun fara karatu,” a cewar Malami, a jawabinsa ga magoya bayansa.
- An Kama Mutane Biyu Da Zargin Safarar Makamai Daga Jigawa Zuwa Katsina
- Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Karin Naira Biliyan 215.3 A kasafin Kudin 2025
Ya zargi magoya bayan Jam’iyyar APC da kai masu hari, “addini ya aminta mu yi wa ’yan uwa jaje in sun samu rashi, shi ne maƙasudin yin wannan ziyara a garin Birnin Kebbi, bakin abubuwa marasa dadi sun bayyana wadanda suke da nasaba da siyasa, bayyane take mutane sun fito daga hedikwatar Jam’iyyar APC ɗauke da miyagun makamai suna jifan abokan hamayya.”
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kebbi Yakubu Ahmed ya ce ba zai ce komai ba kan zargin, magana ce ta jam’iyya don haka a tuntube jami’yya.
Wakilinmu ya tuntubi Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kana a waya amma bai daga ba, ya kuma tura masa sako bai ce komai ba, ya sake kiran sa, amma ya ji ‘number busy.’
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kebbi, Bello Sani, ya ce ba wani da aka kama kan harin da aka kai wa tawagar tsohon minista Malami.
A lokacin da yake magana da manema labarai bayan ya kammala zama da Gwamna kan matslar tsaro, Kwamishinan ’yan sandan ya ce ana gudanar da bincike kan abin da ya faru.

