Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yanfashi da dama waɗanda ba ta faɗi adadinsu ba a garin Tsafe na jihar Zamfara bayan wani hari ta sama.
Mai magana da yawun rundunar,,Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai hare-haren ne kan sansanin ‘yanfashi na Sauri ranar Juma’a bayan tattara bayanan siri.
Ya ce bayanai sun tabbatar da ‘yanbindigar na karakaina a wurin da suka ɓoye shanun sata da ke kan wani tsauni da ke ba su kariya da kuma ajiye kayayyaki.
“An kai hare-hare da dama waɗanda suka dira kan ‘yanfashin da ke yunƙurin guduwa cikin duhun daji, inda aka bi su kuma aka kashe su,” in ji sanarwar.

