• Home  
  • Yan Sandan Jihar Neja Sun Bugi Kirjin Sai Sun Ceto Daliban Da Aka Sace
- Babban Labari - Labarai

Yan Sandan Jihar Neja Sun Bugi Kirjin Sai Sun Ceto Daliban Da Aka Sace

Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran […]

Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru.

Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba.

Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al’umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban.

Ya kuma ce daga bisani za a ɗauki mataki kan hukumomin makarantar saboda ci gaba da karatu bayan umurnin kulle makarantu a yankin saboda barazanar tsaro.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai