• Home  
  • Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi
- Babban Labari - Labarai

Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi

Shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya mai ritaya kuma jigo a jam’iyyar APC, Muhammad Babandede, ya ziyarci iyalan tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Abba Anas Adamu Laushi, wanda ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane. Babandede ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummarsa da kuma abokan siyasarsa, yana mai […]

Shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya mai ritaya kuma jigo a jam’iyyar APC, Muhammad Babandede, ya ziyarci iyalan tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Abba Anas Adamu Laushi, wanda ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.

Babandede ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummarsa da kuma abokan siyasarsa, yana mai cewa marigayin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa jama’a hidima

Yayin ziyarar, ya kai wa iyalan marigayin kayan abinci da tallafin kuɗi domin rage musu radadin halin da suke ciki, tare da tabbatar musu da cewa ƙofarsa a buɗe take a duk lokacin da suke buƙatar taimako.

Ya kuma hori ’ya’ya da magadan marigayin da su ci gaba da riƙo da kyawawan ɗabi’u, karamci da halayen alheri da mahaifinsu ya shahara da su tun yana raye.

Babandede ya yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, tare da bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000