Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar Tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaron Najeriya Manjo-Janar Rabe Abubakar (Ritaya) a hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa shi a jihar.
Kwamishinan Harkokin Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu, ya sanar a ranar Asabar cewa Manjo-Janar Rabe Abubakar ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ’yan bindiga, duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suka yi na tabbatar da an kuɓutar da shi.
Sanarwar ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da ciwon sukari da hawan jini, tana mai bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Gwamnatin ta nuna matuƙar alhini kan lamarin, tana mai cewa sace marigayin da kuma rasuwarsa daga bisani babban rashi ne ba ga iyalansa da jihar Katsina kaɗai ba, har ma ga Nijeriya baki ɗaya.
