• Home  
  • Wani Dan majalisar Jiha Ya Rasu bayan kwanaki 3 da Ranstar da Su a Majalisa
- Labarai

Wani Dan majalisar Jiha Ya Rasu bayan kwanaki 3 da Ranstar da Su a Majalisa

Wani ɗan majalisa mai suna Madami Garba Madami, mai wakiltar mazaɓar Chikun dake jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya rasu bayan kwanaki uku da rantsar da su a majalisar jiha karo ta goma.

Dan majalisar ya rasu ne a yau Asabar 17 ga watan Yuni a asibiti bayan samun kulawar likitoci.

Wani mai mukamin gargajiya a ƙaramar hukumar Chikun, Ibrahim Saleh Ardon Ardodin, ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa.

Dan majalisar ya yi fama da jinya ko da a lokacin da ake rantsar da majalisar karo ta goma a ranar 13 ga watan Yunin shekarar da muke ciki kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Inda rahotanni ke bayyana rasuwar Dan majalisar a matsayin abin alhini, musamman ga al’ummar da yake wakilta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000