Afirka ta Yamma: Ba za mu sake lamuntar juyin mulkin soji ba ~ Shugaba Tinubu

DAGA: ISMA’IL SULAIMAN SANI

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba za su sake yarda da juyin mulki a kasashen Yammacin Afirka ba.

Tinubu ya bayyana haka ne ranar Lahadi jim kadan bayan an zabe shi a matsayin shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS mai kasashe mambobi 15.

Shugaban ya ce, Dimokuradiyya na da wahalar gudanarwa amma ita ce tsarin gwamnati mafi kyau,

Ya kara da cewa: “Babu wani a cikinmu da bai yi yakin neman zabe domin ya zama shugaba ba. Ba mu bai wa sojojinmu kudi da zuba jari a kansu da horar da su don su take ‘yancin jama’a ba…Kada mu zauna a Ecowas kamar kyanwar-lami.”

Sabon shugaban na Ecowas ya kuma yi gargadi kan yadda yankin na Yammacin Afirka ke fama da rashin tsaro sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda.

Ya bayyana cewa ta’addanci da rashin tsaro suna matukar kawo koma-baya ga ci-gaban yankin.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr