Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara jami’ar Near East da ke kasar Cyprus domin jin dalilin hana ɗaliban da gwamnatin jihar ta ɗauki nauyi takardun kammala karatun su.
A wani jawabi da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce, an hana ɗaliban jihar Kano sakamakonsu ne saboda kasa biyan jami’ar haƙƙinta da gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yi ne.
Ya ce “Gwamna ya tattauna da hukumar Jami’ar Near East kan yadda za a karɓo sakamakon ɗaliban da suka yi karatu a tsakanin a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019. Musamman ɗaliban kiwon lafiya.
Sanusi ya ce “Ɗakiban da suka kammala karatu sun kasa fara aiki, tunda basu da shaidar kammala karatu”.
Jawabin na Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce “Wannan rashin biyan kuɗin makarantar da gwamnatin baya ta yi a cutar da yaran mu ƙwarai da gaske, ya hanasu ci-gaba, uwa uba kuma ya cutar da jihar Kano, musamman a dai-dai wannan lokaci da mu ke buƙatar agajin masana kiwon lafiya.
“Abin mamaki ne yadda gwamnatin Ganduje ta yi watsi da wannan nauyi mai matuƙar muhimmanci, musamman lura da cewa muna matuƙar buƙatar likitoci”.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana ganawarsa da hukumar Jami’ar Near East a matsayin mai amfani, wadda za ta haifar da sakamako mai kyau na bai wa ɗaliban jami’ar ‘yan asalin jihar Kano sakamakonsu.