Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai Ta Najeriya IBAN ta naɗa Alhaji Muhammad Babandede OFR muƙamin jagora a tafiyar ƙungiyar ta ƙasa domin neman cigaba da bunƙasa harkokinta.
Alhaji Muhammad Babandede OFR, OCM wanda ya riƙe shugabancin Hukumar Shigi da Fici ta Ƙasa (Immigration) shine mamallakin tashoshin radiyo da talabijin na MUHASA da ke yaɗa shirye-shirye a mita 92.3fm Kano da ta intanet a www.muhasatvr.ng.
Yayinda MUHASA TV ke yaɗa shirye-shirye a tasha ta 170 a dikodar StarTimes.
Alhaji Babandede wanda gogaggen ma’aikaci ne ya samu muƙamin ex-officio a IBAN domin kawo cigaba a harkokin kafafen yaɗa labarai a Najeriya.
Sabon jagoran a IBAN ya sha alwashin bada gudummawarsa musamman wurin yaƙi da labaran ƙarya da ke samun wurin zama a harkokin aikin jarida a Najeriya.