Allah Ya Yi Wa Rajistaran Jami’ar Bayero Rasuwa

Wannan sanarwa wannan rashi da jami’ar Bayero ta yi, ya fito ne daga hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na Jami’ar Bayero Kano, Malam Lamara Garba.

Ya bayyana cewa Rajistaran ya rasu da sanyin safiya ranar Laraban nan.

Inda aka gudanar da sallar jana’iza da ƙarfe goma 10:00 na safe a babban masallacin dake sabon reshen jam’iyyar ta Bayero.

Malam Jamilu Ahmed Salim, ya shafe tsawon shekaru huɗu a matsayin rajistaran Jami’ar kuma Malam Lamara ya bayyana shi a matsayin haziƙi wanda ya ba da gudunmuwa mai yawan gaske ga cigaban jami’ar.

Sannan ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa tare da saka masa da gidan Aljanna.

Post masu alaƙa

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.

Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 daga masu garkuwa a Kogi.

Kotu tsare mutane biyu da ake zargi da rushe Gadar Watari da yanka filaye ba bisa ka’ida ba a Kano.