An Kama Mutane 14 Kan Kisan ’Yan Arewa A Edo
Rundunar ’yan Sandan Najeriya sun ce sun kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo.
Rundunar ’yan Sandan Najeriya sun ce sun kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo.
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da yankunan dake makwabtaka.
Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan mutane 16 da aka yi a jihar Edo, yana mai umartar hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka yi wannan mummunar aika-aikar.
Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso,da tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗantakarar shugabcin ƙasar a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar sun yi tir da kisan ‘yan Arewa a jihar Edo, inda suka nemi a gudanar da bincike.
Ƙungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce mutane 16 aka kashe a mummunan kisan gillar jihar Edo ’yan asalin Kano ne, Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya ta tabbatar da cewa ’yan sa- kai ne suka kai mummunan hari kan waɗansu matafiya ‘yan Arewacin Najeriya, amma binciken farko ya tabbatar da cewa ‘yan sa kan sun zata ɓata gari ne a motar da suka tare.
Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da kashe wasu matafiya ‘yan Arewacin Najeriya da aka yi a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar arewa maso gabashin Esan a ranar Alhamis da ta gabata, wato 27 ga Maris, inda ya bayyana kisan a matsayin na dabbanci. Ana ta dai yaɗa wasu faya-fayan bidiyo, […]
Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda shi ne shugaban Majalisar ƙoli ta addinin Musulunci a ƙasar ya buƙaci al’umma su duba jinjirin watan Shawwal na shekarar Musulunci ta 1446 (Bayan Hijira) a gobe Asabar. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmin ta fitar a yau Juma’a, wadda ta samu […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron jihar sun sanar da dakatar da gudanar da bukukuwan hawan sallah karama. Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori , ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a shelkwatar rundunar yan sandan dake unguwar Bompai a yau […]
Babbar kotun shari’ar musulunci dake zamanta a kasuwar kurmi Kano, ta bai wa mataimakin babban Sufetan ƴan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta ɗaya, ya binciki shugaban jam’iyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Kano, Faizu Alfindiki, kan zarginsu da ɓata wa Gwamnan jihar Kano Abba […]