Jam’iyyar PDP Ta Kafa Kwamitin Shirya Babban Taronta Na Kasa

Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitin da zai shirya babban taron jam’iyyar a ƙarƙashin gwamman Adamawa Amadu Fintiri.

PDP ta ce majalisar zartarwar ta amince da kafa wani ƙarin kwamitin da zai yi nazari a kan tsarin karɓa karɓan muƙamai a jam’iyyar gabanin babban taronta, a ƙarƙashin Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri.

Jamiyyar ta ɗauki wannan mataki ne a yayin zaman majalisar ƙoli da ta gudanar a ranar Talata a birnin Abuja.

A yayin taron, jam’iyyar ta kuma yi Allah wadai da rufe hedikwatarta da hukumar kula da birnin Abuja ta yi, tare da shan alwashin bin kadin matakin.

A ranar Litinin hukumar kula da birnin Abuja, FCTA ta garƙame hedikwatar PDP da aka fi sani da Wadata Plaza saboda rashin biyan harajin ƙasa, lamarin da ya janyo cece ku ce.

Post masu alaƙa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu