Na tabbatar da sahihancin bidiyon Dalar tsohon gwamna Ganduje ~ Muhyi Magaji Rimin Gado
Hukumar karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta ce binciken kwakwaf din da aka gudanar ya nuna bidiyon Dalar da ake zargin tsohon gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje da karbar na goro gaskiya ne.