Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da cewa ta haɗa mutum 146 da aka sace daga ƙauyen Woro da iyalansu bayan sun shafe kwanaki 21 a cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa da farfaɗo da su daga abin da suka fuskanta.
An kai hari ƙauyen Woro ne a ranar 3 ga Fabrairu, inda aka yi garkuwa da mutum 146, kafin daga bisani aka kuɓutar da su a ranar 5 ga Agusta.
Gwamnatin jihar ta kuma ba waɗanda aka kuɓutar tallafin kuɗi, inda manya suka samu naira miliyan ɗaya kowannensu, matasa naira dubu 500,000, yayin da yara suka samu naira dubu 200,000 domin taimaka musu su fara rayuwa ta sabo.
Shugaban ƙaramar hukumar Kaiama, Abubakar Abdullahi Danladi, ya yaba wa Shugaba Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan rawar da suka taka wajen ceto da kuma kula da waɗanda aka sace.
Sai dai shugaban kwamitin da ke hulɗa tsakanin gwamnati da al’ummar Woro, Ahmed Ibn Ahmed, ya ce har yanzu mutum 13 na hannun masu garkuwa da mutane, tare da kira ga gwamnati ta ƙara ƙoƙari domin ceto su.