Amurka Ta Daure Basaraken Osun Kan Zamba A Tallafin COVID-19

Wata kotu a Ƙasar Amurka, ta yanke wa Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, daga Jihar Osun, hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi a gidan yari saboda samun sa da laifin zamba a tallafin COVID-19.

Alƙalin kotun, Christopher Boyko ne, ya yanke wa Sarkin mai shekara 62 a duniya hukunci a ranar 26 ga watan Agusta, 2025.

Bayan ya fito daga gidan yari, zai yi shekara uku ƙarƙashin kulawa, sannan dole ne ya biya sama da dala miliyan 4.4.

Kotun ta kuma ƙwace gidansa da ke Ohio da kusan dala 100,000 da aka samu daga cikin kuɗaɗen da aka yi bincike a kansu.

Waɗanda suka shigar da ƙara sun ce Oloyede tare da abokinsa, Edward Oluwasanmi, sun karkatar da kuɗaɗe wanda gwamnatin Amurka ta samar na rance don taimaka wa kamfanoni a lokacin annobar COVID-19.

Daga watan Afrilun 2020 zuwa Fabrairun 2022, sun gabatar da takardun bogi don samun rance ta hanyar U.S. Small Business Administration (SBA).

Oloyede, ya mallaki kamfanoni da ƙungiya mai zaman kanta, yayin da Oluwasanmi ya mallaki kamfanoni guda uku.

Oloyede, ya shirya takardun bogi 38 da suka ba shi damar samun dala miliyan 4.2.

Haka kuma, ya taimaka wa wasu abokansa wajen samun rancen, tare da karɓar kashi 15 zuwa 20 daga cikin kuɗin da suka samu a ɓoye, ba tare da ya biya haraji ba.

An gano cewa sun yi amfani da kuɗin wajen sayan filaye, gina gidaje, da kuma motoci masu tsada.

Oluwasanmi, wanda shi ma yake da shekara 62, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu da watanni uku gidan yari a watan Yuli.

Sannan kotun ta umarci ya dawo da sama da dala miliyan 1.2.

FBI da wasu hukumomi ne suka gudanar da bincike tare da gano yadda aka tafka zamba a tallafin na COVID-19.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda