’Yan bindigar da suka sace wani mutum da matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa.
Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda.
An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata.
A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su.
- Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ma’aurata Da Yarinya Mai Shekaru 2 A Katsina
- Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane 7 A jihar Zamfara
Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa majiyar mu cewa ’yan bindigar sun kira ɗan uwan Halimat, Malam Ibrahim, ta wayar Anas domin neman kudin fansa Naira Miliyan 600.
Sai dai iyalan sun bayyana cewa ba za su iya biyan wannan kuɗi ba.