An Daure Magidanci Kan Damfarar Tsohuwar Matarsa

Wata kotun Musulunci da ke jihar Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin wata biyu kan damfarar tsohuwar matarsa.

Kotun da ke zamanta a ’Yan Alluna a Ƙaramar Hukumar Fagge, ta yanke hukuncin ne bayan samun sa da laifin bai wa tsohuwar matarsa rasit ɗin bogi na kuɗin abincin ɗansu.

A yayin gurfanar da wanda ake zargin, ya ce a wani shago ne aka buga masa rasit ɗin bogi na Naira dubu hamsin da ya bai wa tsohuwar matar tasa.

Ya shaida wa kotun cewa, a unguwar Mandawari aka buga masa rasit ɗin bogi na Naira dubu hamsin.

Mai Shari’a Khadi Nasir Abdullahi Muhammad, ya yanke masa hukuncin ɗaurin wata uku ko biyan tarar Naira dubu hamsin.

Ya kuma ba da umarnin yi masa bulala 10.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya