Rahotanni daga jihar Borno na cewa wadansu mutane da kawo lokacin rahoton nan ba a san ko su wanene ba sun kwashe kayan abincin wata motar Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak.
Wata Majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana lokacin da Aminu Malam Umar direban wata babbar mota ƙirar Iɓeco ya tsaya a gefen titi.
Yayin da motar ta tsaya a gefen titi ba tare da kula daga jami’an tsaro ba, wasu da ba a san ko su waye ba suka sace buhunan shinkafa da gishiri da sukari da wake da kuma man girki da dama, duk da cewa ba a tantance adadin da kuma darajar kayayyakin da aka sace ba har ya zuwa yanzu.
- Babu Wasu Masu Adawar Da Za Hana Tinubu Cin Zaɓen 2027 — Ganduje
- Ranar Kula Da Tsaftar Baki Ta Duniya 2025
Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, amma ba a kama kowa ba.
Daga bisani sojoji sun ɗauke motar zuwa Gubio lafiya lau a yayin da ake ci gaba da bincike don gano waɗanda suka aikata laifin tare da ƙwato kayayyakin da aka sace.