An dakatar Likitoci 3 saboda barin Almakashi a cikin mara lafiya a Kano

Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta ce ta tabbatar da zargin da aka yi na cewa ma’aikatan lafiya sun bar almakashi a cikin wata mata mai suna Aishatu Umar a lokacin tiyata, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta daga bisani.

Wata sanarwa da ta fitar na cewa Babban Sakataren Hukumar Dr. Mansur Mudi Nagoda ya dakatar da ma’aikatan da lamarin ya faru a lokacin aikinsu tare da gabatar da batun a gaban kwamitin ladabtarwa.

Hukumar ta ce ta dakatar da ma’aikata uku waɗanda suke da hannu a cikin lamarin nan take.

Har ila yau, sanarwar ta ce an miƙa batun ga kwamitin ladabtarwa ga ma’aikatan lafiya a jihar domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace waɗanda dokoki suka tanada.

Hukumar ta kuma miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiya Aishatu Umar kan abin bakin ciki da ya faru.

Ta tabbatar da cewa ba za ta lamunci kowane irin sakaci ba kuma za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kare rayuka da kuma samun amincewar marasa lafiya a faɗin cibiyoyin lafiya na jihar.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda