Wata kotu ta tura matashi mai amfani da shafin Tiktok ɗan shekara 21gidan yari a Uganda bayan ya wallafa wani bidiyo da aka ce yana cin mutuncin shugaba Yoweri Museveni.
Dan Tiktok Emmanuel Nabugodi ya bayyana ne a gaban kotu a ranar litinin, bayan ya amsa laifinsa a makon da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da wasu kalamai na nuna ƙiyayya da yaɗa munanan bayanai game da shugaban ƙasa Yoweri Museveni.
Biyo bayan amsa laifinsa a gaban kuliya, Emmanuel Nabugodi zai yi zaman gidan yari har na tsawon watanni 32.
- An Sace Kayan Abincin Agajin Da Za A Kai Gaza: MDD
- Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Kyandar Biri
Emmanuel Nabugodi ya shahara wurinn wallafa abubuwan barkwanci ga mabiyansa kusan dubu 20.
An ce Emmanuel ya yi wani bidiyon shari’ar izgili da ake yi wa shugaban ƙasa. A ciki ya yi kira da a yi wa Museveni bulala a bainar jama’a.
Wasu Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun yi ta bayyana takacinsu inda su ke korafi kan abin da suka kira tauye ƴancin faɗin albarkacin baki a ƙasar Uganda.
Kungiyoyin suna zargin cewa shugaban wanda ke kan karagar mulki tun shekarar 1986 ba ya lamuntar suka a gare shi ko kuma zazzafar adawa.
Ko a watan Yulin da ya gabata, an yankewa wani Edward Awebwa hukuncin shekaru shida akan irin wannan tuhuma da aka yi wa Nabugodi.
Yayin zartar da hukuncin na Nabugodi, Stellah Maris Amabilis, babbar alƙaliyar kotun Entebbe, ta ce bai yi nadama ba, kuma hukuncin zai taimaka wajen daƙile sukar da ake kai wa mutane a shafukan sada zumunta ciki har da na shugaban ƙasa.