Daga: Mujahid Wada Musa
Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta gurfanar da daya daga cikin matasan da ake zargi da kashe wani dan sanda, mai suna Murtala Auwalu, a kan titin france road lokacin da yake tsaka da gudanar aiki, a ranar 1 ga watan Janairun 2025.
An gurfanar da Abdussalam Lawan ne a gaban wata kotun Majistiri dake zaman ta a unguwar Gyadi-gyadi Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Haulatu Magaji, da tuhumar hada kai don aikata laifi da kuma kisan kai , wanda yin hakan ya saɓa wa sashi na 221 na kundin manyan laifuka, amma wanda ake zargin ya musanta.
Tunda fari ana tuhumar matashin da kuma wasu abokansa wadanda suka gudu, da hannu dumu-dumu wajen kashe jami’in dan sandan.
- Za Mu Yi Yaki Da Shara A Jihar Kano – Dokta Dahiru
- EFCC Ta Kama Jami’an Gwamnatin Katsina Kan Satar Miliyan Dubu 1300
Mai shari’a Haulatu Magaji , ta dage ci gaban sauraren shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Fabarairun 2025, don samun shawarwarin gwamnati sakamakon rashin hurumin kotun.
Iyalan jami’in ɗan sandan da aka halaka sun yi kira ga sarkin Kano, Gwamnan Kano da kwamishinan ‘yan sanda su kara fadada binciken kan wanda ake zargin domin yi mu su adalci.