An tsaurara ƙarin jami’an tsaro a gidan Gwamnatin Jihar Kano a safiyar Litinin a yayin da ake dakon sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Wakilinmu ya lura cewa an girke ƙarin ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS a babbar ƙofar shiga da wasu muhimman wurare a gidan gwamnatin.
- Sojoji sun ceto fasinjojin da aka yi yunƙurin sacewa kan hanyarsu zuwa Kamaru
- Tinubu ya isa Abu Dhabi don halartar taron makamashi
Kazalika an girke motocin yaƙi guda shida mallakin DSS da ’yan sanda kuma an tsaurara bincike da tantance baƙi.
Duk da cewa kawo yanzu Gwamnan bai sanar a hukumance cewa zai sauya sheƙa ba, amma rahotanni sun yawaita cewa yana shirin sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC.

