• Home  
  • An Kama Hon Gudaji Kan Zargin Karɓar Kyautar Miliyan 70 Daga Emefiele 
- Babban Labari - Labarai

An Kama Hon Gudaji Kan Zargin Karɓar Kyautar Miliyan 70 Daga Emefiele 

Rahotanni da yammacin Laraba sun ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta tsare tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar wani yanki a jihar Jigawa, wato Honarul Muhammad Gudaji Kazaure bisa zargin shi da aikata laifukan kuɗi. 

EFCC ta gayyaci Hon Gudaji ne zuwa ofishinta da ke Kano, inda daga bisani ta tsare shi, ana sa za a dauke shi a jirgin sama zuwa Abuja.

Bayanan da manema labarai suka samu sun ce, EFCC tana neman bayanan wasu kyaututtukan kudade naira miliyan 14 da suka shiga asusun ajiyar tsohon dan majalisar a wani lokaci a shekarar 2019.

Sai dai jaridar Daily Nigerian ta ce wasu majiyoyi a EFCC sun bayyana mata cewa ana zargin Gudaji Kazaure da karbar kyautar Naira miliyan 70 daga wurin tsohon gwamnan babban Bankin Najeriya CBN, wato Godwin Emefiele da har yanzu shima ya ke gaban kotu domin amsa wasu tuhume-tuhume.

A baya dai Hon Gudaji Kazaure ya yi ƙaurin suna wurin cacckar tsohon shugaban Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai