Rundunar yan sandan jihar Jigawa, ta kama wani malamin makaranta da zargin da halaka Almajirinsa mai suna Bashir Ahmed, ta hanyar dukansa da Bulala saboda rashin zuwa makaranta ba tare da sanin malamin ba.
kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa SP Lawan Shiisu Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aikewa da manema labarai a jiya juma’a.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargin mai suna , Malam Musa Wada, dan shekaru 45 dake unguwar Jikas-Dabaja, a ranar 13 ga watan Maris 2025.
Idan ba a manta ba a ranar 12 ga watan maris 2025, jami’an yan sandan Gwaram, sun sami rahoton ganin wata Gawa da aka yasar da ita a hanyar garin Jikas-Dabaja, wadda aka cirewa kai da kuma wasu sassan jikinta harma ta fara rubewa, inda jami’an yan sandan suka fara gudanar da bincike akai.
binciken yan sandan ya gano cewar gawar yaron ce mai shekaru 14 a duniya wanda ba a gani ba tsawon kwanaki biyu.
Tuni wanda ake zargin ya tabbatar wa da yan sanda cewa, shi ne ya yanke kan Almajirin da kuma wasu sassan jikinsa don alakanta hakan da yan kungiyar matsafa don kar asirinsa ya tonu saboda kimar da yake da ita a idon al’ummar yankin.
kuma ya yi haka ne lokacin da yake dukan Almajirinsa, bayan ya gaza basa gamshasshiyar amsar rashin zuwansa makaranta , amma bayan ya yi masa Bulala 5 sai yaga ya fadi ko motsi baya iya yi.
SP Shiisu Adamu ya kara da cewa Malam Musa Wada , yana babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan kisan kai na CID dake Dutse, kuma da zarar sun kammala za su gurfanar dashi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.
- Za Mu Kama Duk Wanda Ya Fito Yin Tashe: Yan Sandan Kano
- Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Tallafin Biliyan 16