Home » Za Mu  Kama Duk Wanda Ya Fito Yin Tashe: Yan Sandan Kano

Za Mu  Kama Duk Wanda Ya Fito Yin Tashe: Yan Sandan Kano

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da dakatar da duk wani nau’i na tashe a fadin jihar, sakamakon yadda wasu batagarin matasa suke fakewa suna aikata laifuka.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aikewa da manema labarai a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce wannan ya biyo bayan matakin da gwamnatin Jihar ta dauka, na hana tashe, wanda aka fara a ranar 10 ga watan ramadan, sakamakon yadda wasu batagari suke fakewa da sunan tashen, inda suke yi wa mutane fashin kayayyakinsu da kuma yi musu ta’adi na dukiyoyi.

Rundunar ta kara da cewa duk wanda aka kama ya fito da sunan yin tashe, ko shakka babu jami’an tsaro za su kama shi tare da binckarsa sannan a gurfanar dashi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.

MUHASA Radio, ta ruwaito cewa rundunar yan sandan, ta yi zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki, na unguwannin Yakasai, Zage, Zango da kuma Rimi don gannin an magance duk wani nau’i na fadan daba a fadin jihar.

Taron masu ruwa da tsakin ya hadar da shugabannin al’umma, Dagatai, masu Unguwanni, yan kwamitocin tsaro da Yan bijilanti da kuma jami’an Yan sanda.

SP Abudullahi Kiyawa, ya ce an shirya taron ne don tattaunawa kan yadda za a magance fadan daba da yake yi wa al’ummar jihar barazana.

Haka zalika binciken rundunar yan sandan,  ya gano cewar shan kayan maye da kuma siyarwa ne yake haifar fadan daba, inda rundunar ta kudiri aniyar zakulo batagarin da ake zargi da aikata,  aika-aikar fadan daba da kuma masu siyar da kayan mayen don hukunta su.

Kwamishinan yan sandan jihar, yaja hankalin mataimakansa da kuma Baturen yan sanda, su kara fada sintiri don magance fitowar  batagarin, sannan kuma ya yi kira ga al’umma su ci gaba da basu hadin kai musamman wajen basu bayanan sirrin da zai taima musu na tabbatar da tsaro.

A karshe rundunar ta ce duk lokacin da aka ga wani abun zargi daba a amince dashi ba, a yi gaggawar sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace ko kuma a kira lambobin waya 08032419754, 08123821575 , 09029292926

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?