166
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Abuja ta kama wata mota makare da ƙananan yara har 59 da ake zargin an sato su daga Arewacin Najeriya.
’Yan sandan sun bayyana cewa yaran basu wuce ‘yan shekara huɗu zuwa 12 ba a cikin wani yanayi na dauda.
kawo lokacin hada wannan rahoto babu wani cikakken bayani dangane da halin da yaran ke ciki da kuma ainihin wuraren da aka debo su.