Wasan dambe na daya daga cikin wasanni 48 da ake da su a duniya kuma wasa me mai cikakken asali tun iyaye da kakanni a yankunan da ake yinsa.
Sannan damben gargajiya wani wasa ne da mutane biyu ske nada zare ake naushi ko dukan juna har sai mutum ya fadi kasa sannan za ace an samu nasara a kansa.
Akwai bangarori da dama a fannin damben na gargajiya da suka hadar da Guramada da Jamus da kuma Kudawa.
A can shekarun baya mafi yawa duk wanda ya fito daga yankin Sokoto da Kebi da Zamfara to babu makawa su ake kira da Guramada bazakaga wani bare ba a cikinu, haka ma suma sauran wadanda suka fito daga sauran yankunan ana kiransu da Kudawa da kuma Jamus.
A can shekarun baya a yankunan Zamfara da Kebbi da Sokoto yaro ma ya kan fafata dambe da kanin mahaifinsa ko kakansa amma na wasa ko da kuwa a hanyar gona suka hadu.
Haka zalika a kan hada yara tun suna kananu aga sun taso suna dambe a tsakaninsu domin nuna mazantaka da kuma kwarewa a fannin damben gargajiya.
An yi manyan ‘yan damben da baza a taba mantawa da su ba bayan sun kafa manya manyan tarihi wajen yin kisa a gasar ta damben gargajiya.
Sai dai idan akace kisa a dambe ana nufin idan aka naushi mutum ya fafi ba wai a kashe shi har lahira ba kamar yadda wasu da yawa suke tunani.
Sai dai a ‘yan shekarunnan an zamanantar da gasar ta dambe inda ake zuba kudi a sabgar wajen sanya gasa tsakanin ‘yan wasan na dambe da kuma baiwa wasunsu albashi sabanin shekarun baya.
Haka zalika dan damben da yake a bangaren Guramada zai iya komawa bangaren Jamus, sannan na Jamus zai iya komawa Kudu, haka zalika shima na Kudu zai iya komawa bamgaren Guramada.
Akan yiwa ‘yan wasan dambe ajo a gidajen dambe daban-daban da ake dasu inda ake haduwa a taramusu kudi.
Yanzu an shigo da sababbin dokoki a gasar ta yadda idan dan wasa yayi laifi akan dakatar da shi ko kuma a ci shi tarar kudade ko a hadamasa duka guda biyun.
Yanzu haka ana ci gaba da zamanantar da wasan na dambe inda ko yaushe ake samun ci gaba a sassan da ake gudanar da wasannin na damben garhajiya.