Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya ta tsaurara tsaro gabanin Babbar Sallah

Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya dake jihar Kano, ta bayyana cewa ta ɗauki tsauraran matakan tsaro, kamar yadda babban sufeton ƴan sadan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayar da umarni, don tabbatar da an gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.

Mataimakin sufeton ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya, AIG Garba Ahmed, ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Hussaini, ya rabawa manema labarai ranar talata.

Sanarwar ta buƙaci jama’ar shiyar da suka haɗa da jahohin  Kano da Jigawa, su kasance masu masu bin doka da oda da kuma baiwa jami’an tsaro haɗin kan da yadace don wanzar da zaman lafiya.

Mataimakin sufeton ƴan sandan, ya taya al’ummar musulmin shiyyar murnar bikin babbar sallah ta shekarar 2026.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai