Hukumar Road Safety Za Ta Ɗauki Tsattsauran Matakai Kan Masu Tuƙin Ganganci A Kano.

Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kano, ta ƙudirin aniyar ɗaukan tsattsauran mataki ga duk wanda aka kama da laifin yin tuƙin ganganci a lokutan bukukuwan babbar sallah.

Jami’in hulɗa da jama’a da wayar da kai na hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kano, CRC Abdullahi Labaran, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da gidan telebijin da radio na Muhasa.

Ya ce hukumar ta tanadi jami’anta 1,889 waɗanda za a ajiye wurare dabam-daban tare da kayan aiki da suka haɗa da motocin sintiri guda 24 da motoci masu janye ababen hawan da suka lalace akan hanya da sauransu.

Kazalika ya ce sun tanadi motocin ɗaukar marasa lafiya da inda aka yi hatsari guda biyar da sauran babura da ake yin amfani da su,wajen yin sintiri akan tituna.

CRC Abdullahi Labaran, ya ce suna ci gaba da sanya ido kan wasu manyan laifuka musamman tuƙin wuce sa’a da tuƙin ganganci ko yin lodin daya wuce ƙima da aron hannu ko amfani da wayar hannu.

Hukumar ta ce ba zata yadda da tuƙin ƙananan yara ba, kuma zata ɗauki matakin daya dace.

A ƙarshe hukumar taja hankalin jama’a musamman iyaye kar subar ƴaƴansu suna zirg-zirga sakaka akan tituna.

Post masu alaƙa

Ƴan sandan Kano sun ƙwato motocin sata 3 tare da kama mutane uku da ake zargi

Majalissar dinkin duniya ta ce miliyoyin mutane a Najeriya na iya fuskantar matsananciyar yunwa

Ebola: An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Congo