Shugabannin Ƙungiyar da ke fafutukar haɗe kan magoya bayan ‘yan siyasa a jam’iyyu daban-daban a Jihar Kano da aka yi wa laƙabi da Kwandon Koli ta kawo ziyarar aiki tashar Rediyo da Talabijin na MUHASA.
Shugabannin Kwandon Koli ƙarƙashin jagorancin Honarabul Yakubu Dan Gowan Jingau sun bayyana godiya ga tashar MUHASA bisa gudunmawar da da ta ke bayarwa wurin wayar da kan jama’a akan siyasa da ci gaban al’umma.
Honarabul Dan Gowan ya bayyana cewa akwai ‘ya’yan dukkanin jamiiyyun siyasar Najeriya a cikin ƙungiyarsu, kuma babban burinsu shine kawar da siyasar banga da tumasanci.
Ya ce, “lokaci ya yi da za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin yaƙi da siyasar kuɗi, jahilci da tashin hankali.
“Ba ma tare da wanda bai son zaman lafiya, mun dubi halin da ake ciki musamman a Arewacin Najeriya shi ya sa muka ƙirƙiro wannan tafiya.
Dan Gowan ya ce, lokaci ya yi da za a kaucewa siyasar in ba ni ba kowa ya rasa.
Ya kuma bayyana cewa duk ɗan ƙungiyar su yana da sana’a, ba siyasar kaɗai suka sa a gaba ba.
Magatakardar harkokin kuɗi na ƙungiyar kwamared Nura Muhammad Dakata ya jinjina wa shugabancin tashoshin MUHASA da ma’aikatansu.
Ya ƙara da cewa “‘Yan jarida aikin Allah ku ke yi, muna fata za ku bamu goyon baya domin cimma burin mu”.
Da take nata jawabin, shugaban tashoshin MUHASA Hajiya Aishatu Sule ta jinjinawa shugabannin ƙungiyar bisa yunƙurin kawo gyara a harkar siyasa.
Ta ce, “Manufofin ku abin koyi ne, kuma abin alfahari ne. Da za a yi koyi da irin aƙidar ku da an zauna lafiya.
Ta kuma ƙara da cewa, “Aƙidar ku ta tabbatar da zaman lafiya da cigaban al’umma ta yi kama da ta MUHASA”
Mataimakiyar shugabar tashoshin MUHASA, Hajiya Halima Djimrao ta jinjinawa shugabannin ƙungiyar bisa yunƙurin kawo gyara a harkokin siyasa da zamantakewa tsakanin magoya bayan ‘yan siyasa.
Ta yi kira ga shugabannin da su ji tsoron Allah, su kuma tsayu kan gaskiya da rikon amana.