Gwamnatin jihar Katsina ta ce rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro ta yi nasarar kashe ƴan bindiga 18 a yankin ƙaramar hukumar Dutsinma.
Rahoton ya ce jami’an tsaron sun yi nasarar hallaka ɓarayin ne yayin da suka afkawa wasu ƙauyuka a yankin na Dutsinma.
Gwamnatin ta ce an samu wannan nasarar ne a Jiya asabar, bayan samamen da jami’an tsaro suka kai, sakamakon bayanan sirri da suka samu a kan ayyukan ƴan bindigar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dokta Nasir Muazu, ya ce an kuma samu nasarar karɓo shanu da wasu dabbobi daga hannun ‘yan ta’addar.
“an kuma samu bindiga AK47 da ƙunshik harsashi 11.”
Dokta Nasiru Muazu ya ce an samu sauƙin matsalar tsaro a wasu ƙananan hukumomi idan aka kwatanta da halin da ake ciki a kwanakin baya.