Home » Dole Mu Sulhunta Ganduje Da Kwankwaso – Kofa

Dole Mu Sulhunta Ganduje Da Kwankwaso – Kofa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Abdulmumin Jibrin Kofa Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji dags Jihar Kano, ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakanin manyan ’yan siyasar jihar biyu, Dokta Rabiu Musa Kwanwaso da Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Ɗan Majalisar wanda shi ne shugaban kwamitin gidaje na majalisar wakilai ta Najeriya, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a Kano da su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin shiga tsakani har a samu maslaha tsakanin tsofaffin gwamnonin jihar.

Kofa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyo na Aminci, inda ya ce rikicin da ke tsakanin manyan jagororin siyasar jihar bai dace ba, kuma jihar ce take shan wahala.

“A matsayinmu na musulmi, ya zama wajibi mu shiga tsakani. Sun kasance abokan juna, kuma sun yi abubuwa da dama a tare.

“Abin da ke faruwa a tsakaninsu a yanzu abin takaici ne. Yanzu lokaci ya yi za a haɗa kai a zauna lafiya.

Kofa ya ce ko da ba za su haɗu a inuwar siyasa ɗaya ba, zai yi kyau su riƙa halartar sha’anin juna.

“Mu ga Kwankwaso yana halartar auren ’yar Ganduje, shi ma Ganduje yana halartar auren ɗan Kwankwaso. Idan an yi wa Kwankwaso rasuwa, Ganduje ya je ta’aziyya. Idan an yi wa Ganduje rasuwa, Kwankwaso ya je ya jajanta.

“Maganar siyasa idan sun ga dama su haɗe ko kuma kowa ya yi tasa, amma a yi siyasar bisa ƙa’idar Musulunci.

“Idan sun yi [adawa] a siyasa wannan ra’ayinsu ne, kowa ya yi nasa, amma shirya su, wannan nauyi ne a wurinmu,” inji Kofa.

“Duk mutumin da yake bin rigingimu da ake yi a Kano, ya san tana da alaƙa da rashin jituwar da ke tsakanin jagoranmu [Kwankwaso] da Ganduje.

“Duk da dai har yanzu ’yan NNPP ne mu, muna tare da Kwankwaso saboda mu Kwankwasawa ne.

“Saboda haka tilas ne, amma ba don kar a ce na yi rashin kunya ba, duk da dai lamari ne tsakanin ɗa da uba, amma da sai na ce ko suna so ko ba sa so sai mun yi duk abin da za mu yi iya ƙarfinmu don ganin mun daidaita Kwankwaso da Ganduje.

“Duk wani mutumin kirki a Kano, ya san cewa ya kamata kowa ya zo a haɗa hannu mu ga yadda za a yi a daidaita Kwankwaso da Ganduje.

“Abokai ne, sun daɗe tare da juna, sun yi abubuwan arziki tare sun zama aminan juna, sai wani lamari ya zo ya shiga tsakaninsu saboda haka abu ne mai ciwo a ce wanda ka ɗauka a matsayin amini ya yi maka wannan abu da ba ka yi tsammanin zai yi maka ba.

“Saboda haka ina kiran duk wani mai ra’ayi irin nawa da ya zo a hannu domin daman mun fara wannan yunƙuri domin sulhunta su.”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?